Rahotanni daga yankin Zungeru ta karamar hukumar Wushishi na nuna cewa wani gumurzu aka tabka tsakanin gamayyar jami'an tsaron sojoji Najeriya da kuma 'yan banga a dai dai lokacin da 'yan bindiga ke kokarin tsallaka babban titin kusa da kauyen kundu,
Wani shaidan gani da ido da ya bukaci a sakaya sunanshi yace an dauki tsawon lokaci ana jin karar harbe-harben bindigogi yayin da ake tafka ruwan sama a wannan yanki amma daga bisani jami'an tsaron suka samu galabar fatattakar yan fashin dajin.
Shima wani mazaunin kauyen Kundu da ya nuna a boye sunanshi yace tun a ranar Talantan din da ta gabata suka rika jin labarin tunkaro 'yan fashin dajin amma sai a ranar laraban kwatsam suka fado garin kuma "cikin ikon Allah jami'an tsaronmu sunyi nasara akansu"
Gwamnatin jihar Neja dai tace duk da wannan nasara da aka samu akan wadannan yan ta'adda za'a ci gaba da kara daukar matakan kare duk wani matakin ramuwar gayya daga 'yan bindigar.
Kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Neja, Janar Abdullahi Bello Muhammad Mai ritaya, yace har yanzu basu tantance yawan 'yan bindigar da aka hallaka ba amma zuwa nan gaba zasu kammala bincike.
Har ya zuwa lokacin hada wannan rahoto dai babu wani karin haske daga rundunar 'yan sanda ta jihar Neja akan wannan lamari domin kuwa kokarin samun kakakin yansandan jihar Wasiu Abiodun ta wayar salulu yaci tura.
Saurari rahoton Mustapha Nasiru Batsari:
Dandalin Mu Tattauna