Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga Sun Hallaka Mutune 21 a Jihar Neja


Yan bindiga
Yan bindiga

Kimanin mutane 21 ne ‘yan bindiga su ka hallaka da yammacin ranar Alhamis a jihar Nejan Najeriya.

Bayanai daga yankin Madaka ta karamar hukumar Rafi na nuna cewa, maharan sun abka garin Madaka a dai-dai lokacin da ake hada-hadar cin kasuwa inda suka bude wuta ga al’ummar yankin.

Wasu mazauna garin na Madaka da suka bukaci a sakaya sunansu sun bayyana cewa, bayan kashe mutanen sun bankawa kasuwar wuta inda baburan da motoci suka kone kurmus.

Wasu motoci da aka kona
Wasu motoci da aka kona

Hakimin garin Alh. Isa Bawale yace daga cikin wadanda 'yan bindigar suka kashe har da dagacin garin sannan sun wuce da mutane da dama da kawo lokacin hada wannan rahoton ba a tantance yawan su ba.

Duk kokarin jin ta bakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Neja a kan wannan hari yaci tura.

Haka zalika babu wani karin haske daga Gwamnatin jihar Nejan a kan wannan lamari. Muryar Amurka ta kasa samun wayar kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Janar Bello Abdullahi Muhammad mai ritaya.

Saurari rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:01 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG