MINNA, NIGERIA - Ita ma dai Gwamnatin jihar Nejan ta ce ta yi maraba da wannan ci gaba da aka samu a yaki da ‘yan bindiga da suka addabi jihar.
A wata sanarwa da rundunar sojin saman Najeriya ta fitar mai dauke da sanya hannun kakakinta, Air Vice Marshal Edward Gabkwet, ta ce sun samu nasarar lalata manyan abubuwan fashewa tare da bindigogi wanda aka yi imanin cewa mallakar daya daga cikin ‘yan ta’addan da ake nema ne ruwa a jallo a kasar.
Wasu daga cikin mazauna yankin da lamarin ya faru da suka bukaci a sakaya sunansu sun ce garin Palale nan ne mazaunin wani rikakken ‘dan bindiga mai suna Dogo Gide da sauran mukarrabansa.
Kwamishinan Tsaron Cikin Gida na jihar, Janar Bello Abdullahi Muhammad mai ritaya, ya tabbatar da aukuwar lamarin kuma ya ce za su ci gaba da yaki da bata garin amma kuma suna bukatar hadin kan jama’a.
Mai sharhi kan al’amurran tsaro a Najeriya, Dr. Yahuza Ahmed Getso, ya ce duk da yake suna da tabbacin Dogo Gide baya wannan wuri a lokacin da sojoji suka kai harin, amma wannan babban sako ne gare shi.
Yankin na Shiroro dai ya dade da zama wata matattara ta ‘yan bindiga da hukumomin jihar Nejan suka tabbatar da cewa harda mayakan kungiyar Boko Haram.
A saurari cikakken rahoto daga Mustapha Nasiru Batsari:
Dandalin Mu Tattauna