A kalla mutane 4 suka mutu wasu guda 20 shuka ji raunuka sakamakon wani jerin harbin bindigar da aka yi a jihar Kansas da ke tsakiyar yammacin Amurka. Jami’an tsaro sun ce dan bindigar na daga cikin wadanda aka kashe.
A jerin harbin da aka yi a wurare daban-daban a kusa da birnin Hesston din jihar ta Kansas a ranar Alhamis din ta jiya. Maharbin bindigar an bayyana cewa ma’aikaci ne a wani babban kamfani.
Wani jami’in dan sanda mai suna T. Walton ne ya bindige shi maharin. Dan sandan yace bashi da abin fada akan lamarin sosai da aka tambaye shi. Hesston dai dan karamin gari ne da yake da yawan mutane kimanin 3,700 mazaunansa. Yana da nisa kamar kilomita 56 daga Arewa da garin Wichita.