Kirkire-kirkire kan tallafa ma rayuwar dan adama da taimakama tattalin arzikin kasa. Ba abun mamaki bane aga cewar duk mutane da suka kirkiro wasu abubuwa a rayuwar yau da kullun, suke zama mutane na farko da kan fara gwada amfani da wannan abun da suka kirkiro.
Sau da dama kuwa wadannan abubuwan da suka kirkira kan zamo sanadiyar mutuwar su. Ga kadan daga cikin masana kimiyya da fasa, da suka kirkiri wasu abubuwa a rayuwar su, kuma wadnnan abubuwan suka zama sanadiyar mutuwar su. Mr. Francis Edgar Stanley, da kanin shi sun kirkiri wata mota a shekarar 1896, wanda a wannan lokacin suka yi abun tarihi a duniya, wanda motar tasu tazama mota da tafi kowacce mota gudu. A shekarar 1918 Mr. Francis, yana tafiya cikin motar tashi kirar su shi da kanin shi, sai motar ta bugi wani ice ya mutu.
A shekarar 1783 Mr. Jean-Francoise Pilatre, shine mutun na farko da ya kirkiri Kunbo-Afolo jirgin dake yawo a sararin samaniya da wutar murhu, bayan samar da wannan kunbon, wasu mutane biyu sunyi kokarin wuce tekun maliya sai suka kasa, shi kuwa Mr. Jean, yayi yunkurin wace tekun na maliya, sai kunbon yazama ajalin shi.