Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rikicin Kabilanci A Habasha Yayi Sanadiyar Asarar Rayuka


Kasar Ethiopia, wato Habasha na huskantar wani sabon rikici a bakin iyakar ta, dake yammacin kasar.

Rikicin wanda ya fara a farkon watan Janairu, ya fara ne a matsayin rikicin fili tsakanin ‘yan kabilar Nuer da na Anyuak, amma yanzu ya bazu kuma yayi dalilin mutuwar mutane da dama.

Wannan rikicin dai ya samo asali ne sakamakon kwararowan yan kabilar ta Nuer wadanda yakin kudancin Sudan ya raba da muhallin su, abinda ya tilasta su kwarara zuwa yankin gundumar Gambella dake kasar ta Ethiopia.

Rahotanni sun bayyana cewa wadannan yan kabilar ta Nuer sun iso wannan wurin da suka yi dafifi, sun iso da makamai musammam bindigogi, kuma koda suka zo suka ki zama lafiya sai suka kara tada hayaniya ga al’ummar da can daman tana zaman dar-dar.

Kamar yadda hukumar kula da ‘yan guudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya tace akwai yan gudun hijira da yawan su yakai Dubu 280, kuma da yawan su yan kudancin Sudan ne, wadanda kashi 84 daga cikin su suna zaune ne a sansanin na yan gudun hijira kana kashi 16 na zaune da ainihin mutanen da suka taras a gundumar ta Gambella.

Obang Metho shugaban wata kungiya mai zaman kanta na kasar ta Ethiopia yace a kalla mutane da yawan su yakai 50 ne suka mutu sakamakon wannan fada tsakanin wadannan kabilun biyu.

Yace kuma yayi imanin ba kome ne ya kawo fadan tsakanin suba illa rikicin fili.

XS
SM
MD
LG