Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Ci Gaba Da Zaman Dar Dar Game Da Cutar ZIKA

A pregnant woman holds a mosquito net in Cali, Colombia, Feb. 10, 2016. The Colombian Health Ministry began delivering mosquito nets for free to pregnant women to prevent the infection by Zika virus, vectored by the Aedes aegypti mosquito.

Ana ta ci gaba da zaman dar-dar game da cutar nan ta ZIKA mai nasaba da haifar da matsala ga jarirai sabbin haihuwa. Inda shugabar Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce cutar na iya kai kololuwar matsala kafin a iya shawo kanta. Ta fadi haka ne bayan tattaro bayanan cutar da aka kudura a Brazil.

Dakta Margaret Chan, ta kira wannan cuta ta ZIKA a matsayin mai hatsari fiye da cutar Ebola da ta hallaka sama da mutane Dubu 11 a Afirka. Cutar dai ta ZIKA dai tana haddasa haifar jarirai da kananan kai ko makamancin hakan.

Dakta Anne Schuchet ma ta Hukumar shawo kan cututtuka ta Amurka, ta bayyana cewa akwai bukatar sai an kara himma wajen bada kudaden da za a yi amfani da su wajen aiwatar da binciken makarin cutar ta ZIKA da ta samo asali daga kasashen Kudancin Amurka.

XS
SM
MD
LG