Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kama Mutumin Da Ya Kai Hari Birnin Kalamazoo Ya Kashe Mutane 6


Kalamazoo Shootings
Kalamazoo Shootings

Hukumomi sun ce sun tsare wani da ake zargi da bude wuta ya kashe mutane shida wadansu biyu kuma suka ji raunuka a jihar Michigan dake arewacin Amurka.

‘Yan sanda sun bayyana jiya Lahadi cewa, sun kama Jason Dalton dan shekaru 45 direban kamfanin motar hayar ne da ake kira Uber. Jami’ai sun ce iya saninsu, ba a taba samunshi da wani laifi ba.

An kai harin ne a ranar asabar wajen birnin Kalamazoo.

Hukumomin sun ce tashin hankalin ya fara ne a wasu gidajen kwana inda aka jiwa wata mata da aka harba sau biyu mummunan rauni. Bayan
‘yan sa’oi kuma, dan bindigan ya kashe wani mutum da dansa dake duba mota a wajen sayarda motoci.

Mintoci bayan nan, ya harbe mutane biyar a wajen ajiye motoci dake wurin wani cin abinci. Hudu daga cikinsu sun mutu. Wata yarinya ‘yar shekaru hudu wadda da farko aka ce ta mutu, tana kwance a asibiti da munanan raunuka.

Ba a fadi musababin hare haren ba. Kafofin sadarwa sunce mai yiwuwa Dalton ya sauke wani fasinjan Uber tsakanin lokacin da ya kai hare haren.

Mai shigar da kara na karamar hukumar Kalamazoo Jeff Getting yace za a tuhumi Delton da laifukan kisa da kuma yunkurin kisa idan aka gurfanar dashi gaban kotu yau Litinin.

XS
SM
MD
LG