Shahararren kamfanin wayar hannun nan Apple dake Amurka ya shigar da koke a gaban Kotu don a dakatar da umarnin da kotun tarayya ta bayar na cewa sai sun bude makullin sirrin wayar maharin nan da ya kashe mutane a garin San Bernardino na nan kasar.
Bukatar yin haka shine don leko asirin wayar da kila akwai wata barazanar tsaro a cikinta. In ba’a manta ba dai wani ‘dan ta’adda Syed Rizwan Farook da matarsa ne suka bindige mutane har lahira, tare da raunata wasu bara a jihar ta California, inda daga baya shima aka bindige shi a musayar wuta.
Lauyoyin kamfanin Apple sun nuna cewa idan aka yi haka don leko bayanan wayar maharin wacce kirar Apple 5c ce to an sabawa dokar kamfanin ta farko game da kare sirrin abokan cinikayyarsu. Su kuma jami’an tsaron na FBI sun ce suna so ne saboda magana ce ta tsaron kasa.