Wani Limamin Kirista Ya Soki Hukumomi Kan 'Yan Matan Chibok

Wani malamin addinin kirista pastor Tunde Bakare dake birnin Lagos, wanda ya taba zama dan takarar mataimakin shugaban kasa na Muhammadu Buhari karkashin jam'iyyar CPC a shekarar 2011, ya soki hukumomin Najeriya kan abinda ya kira tafiyar hawainiya wajen kwato 'yan matan Chibok 219 da 'yan Boko Haram suka sace kusan shekaru biyu da suka gabata.

Paston, wanda ya jagoranci addu'oi na cikar 'yan matan shekaru biyu da sacewa yace akwai bukatar gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta tashi haikan wajen ceto yaran na Chibok cikin gaggawa, ta haka ne kawai iyayen wadannan yara da sauran jama'a zasu ga kokarin gwamnati.

A ranar sha hudu ga wannan watan ne 'yan matan na Chibok zasu cika shekaru biyu da sacewa kuma kawo yanzu babu labarin su, kuma tuni gwamnatin tarayya ta fito ta musanta wani rahoto da ake bazuwa cewar kungiyar Boko Haram ta bukaci gwamnatin Najeriya ta biya ta zunzurutun kudi har Naira biliyan goma a matsayin kudin fansa domin a sako 'yan matan da aka sace.

Ga cikakken rahoton da Babangida Jibrin daga Lagos