Jose Mourinho ya musanta zargin da akai masa na rattaba hannu akan kwangilar daukar jan ragamar kungiyar kwallon kafa ta Manchester United a karshen kakar bana.
An shafa ma tsohon manajan kungiyar ‘yan wasan Chelsea mai a baki domin maye gurbin Louis Van Gaal koda shike akwai rade radin cewa Mourinho ya rattaba hannu akan yarjejeniyar amincewa da karbar kwantaragi da kungiyar kwallon kafa ta Red Devils lamarin da ya musanta.
A hirar su da kafar sadarwar Sky Sports, ya bayyana cewa Van Gaal aboki sa ne, kuma sun yi aiki tare na ‘yan wasu shekaru.
Ya kara da cewa “a kullum ina da sukunin samun aiyuka, kuma da bazara zan sami aiki, dan haka ina mai tabbatar maka da cewa a yanzu haka babu wata kwangila dana sa ma hannu da kowacce kungiya”.
Ya cigaba da cewa “bana matsayin da zanki karbar aiki idan aka bani, abinda zan yi shine na duba aikin sosai kuma a yanzu haka kasuwata a bude take ga duk wata kasa ko kungiya da zata dauke ni aiki.”
Mourinho ya jaddada cewa ya fi shi’awar cigaba da gudanar da aiyukan sa na Premier League.
Ya ce “maganar gaskiya anan ita ce idan ina da zabi, to tabbas zan zabi kungiyar da sai na tabbatar da ta cancance ni domin inyi amfani da dukkan irin hazakar da nake da ita.
Zan fi son in zauna a ingila, ina son kasar kuma ina matukar kaunar wasan kwallon kafa a nan, kuma hankalin iyali na a kwance yake”.
Facebook Forum