Ya yi karatu a jami'ar Bayero ta Kano da Jami'ar Maiduguri da ke jihar Borno.
Alkali Baba ya shiga aikin dan sanda a shekarar 1988 a matsayin mataimakin Sufuritanda na ‘yan sanda wato ASP, inda ya kai matsayin kwamishinan ‘yan sanda a ranar 27 ga watan Janairun 2014 inda aka turashi jihar Delta.
Ya kuma rike mukamin Kwamishinan ‘yan sanda a jihar Anambra da babban birnin tarayya Abuja, haka kuma ya yi Kwashinan ‘yan sanda mai kula da tasoshin jiragen kasa.
Karin bayani akan: Usman Alkali Baba, DIG, Mohammed Abubakar Adamu, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.
Alkali Baba ya yi ta samun karin girma inda ya zama mataimakin Sufeto Janar wato AIG na ‘yan sandan Ruwa, wato Police Maritime a jihar Legas da kuma na shiyya ta biyar mai kula da Jihohin Edo da Delta da kuma Bayelsa.
Ya kuma taba zama sakataren rundunar ‘yan sandan Najeriya.
Daga nan ya samu karin girma inda ya zama mukaddashin Sufeto Janar da ake kira DIG, ya kuma rike sashen kudi da mulki na rundunar ‘yan Sanda, sai kuma sashen binciken manyan laifuka na hedikwatar rundunar da ake kira Force CID, kafin wannan mukami da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada shi na mukaddashin shugaban ‘yan andan Najeriya baki daya.
Ranar Talata 6 ga watan Afrilu ne, Ministan hukumar kula da sha’anin ‘yan sandan kasar Maigari Dingyadi ya fadawa manema labarai wannan sauyi a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Fadar shugaban kasar ta ce nadin da shugaba Buhari ya yi wa Usman Alkali Baba (DIG) a matsayin zai fara nan take ba tare da bata lokaci ba.