Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Matsalar Tsaro, Korona Suka Shafi Bukukuwan Easter a Najeriya


Yadda Kiristoci Suka Gudanar Da Bukukuwan Easter A Jihar Kano
Yadda Kiristoci Suka Gudanar Da Bukukuwan Easter A Jihar Kano

Yayin da mabiya addinin Krista a fadin duniya ke kammala shagulgulan bikin Easter wato ranar tunawa da gicciyewa da kuma tashin Yesu Almasihu daga cikin matattu a ranar Litinin.

Shugabannin Mabiya addinin Kirista a Najeriya sun bayyana mahimmacin wannan rana da kuma yadda ta iskesu a wannan shekara ta 2021, tare da jaddada muhimmacin addu’a a lokacin bikin.

Pastor Simon AS Dolly tsohon shugaban matasa mabiya addinin Kirista a Najeriya ya bayyana cewa a bana bikin wanda aka saba gudanarwa a duk fadin duniya bai zo da armashi ba sakamokon yanayin da ake ciki na matsalar tsaro a kasar.

A wani bangaren Root Agnes ta bayyana cewa duk da kalubale na annobar Cutar Covid-19 a Najeriya wanda ya takaita gudanar da shagugulan bikin a shekarar da ta gabata tare da dagula lamura da dama a kasar.

Sai dai ta ce abin godiya ne cewa, duk da wadannan matsaloli, abin godiya da ne mutum ya kasance a raye.

Pastor Yohanna Buru shugaban farfado da zaman lafiya da sasantawa tsakanin mabanbantan addinai a Najeriya ya yi kira tare da jaddada cewa sai an hada hannu wajen samun mafita a halin kunci da kasar ta tsinci kanta a ciki

Gwamnatin Najeriya ta bakin Ministan tsaronta Manjo janar Bashir Magashi ya roƙi Kiristoci da su yi amfani da wannan dama wajen yi wa sojojin ƙasar addu'a don kawo ƙarshen ta'addanci da ya addabi kasar.

XS
SM
MD
LG