Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sanda Sun Kashe Gaggan Dan Bindiga A Zamfara


Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta ce ta sami nasarar kashe wani shahararren dan bindiga da ya kware a sha’anin satar mutane da sauran ayukan ta’addanci a yankin karamar hukumar mulki ta Maradun.

A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ta Zamfara SP Muhammad Shehu ya fitar, ta ce dan ta da kayar bayan da aka kashe ya dade a cikin jerin sunayen gaggan ‘yan ta’addar da jami’an tsaro ke bukata, duk da yake bai bayyana sunansa ba.

Sanarwar ta ce lamarin ya auku ne a ranar 4 ga watan Afrilun nan, sa’adda jami’an rundunar Puff Adder kashi na biyu suke sintiri a kan titin Tsibiri da ke kusa da dajin Sububu, a cikin karamar hukumar mulkin Maradaun.

SP Muhammad ya ce rundunar ta sami nasarar tarwatsa gungun wasu ‘yan bindiga da ke kan hanyarsu ta kai harin ta’addanci a kauyen na Tsibiri.

'Yan Sanda A Jihar Zamfara
'Yan Sanda A Jihar Zamfara

Ya ci gaba da cewa “amma da suka hangi ‘yan sanda, sai suke bude wuta, yayin nan take su ma ‘yan sanda suka mai da martani, wanda yayi sanadiyyar kashe dan bindigar daya, yayin da na biyun ya sami arcewa da raunin harbin bindiga a jikinsa.”

Sanarwar ta ce an sami karbe bindiga kirar AK-47 mai lamba AK 103 2051361627, da kuma gidan harsasai daya, da babur da kuma wata jaka mai dauke da tufafin kakin soji, kazalika da layu.

Jihar ta Zamfara dai ta dade tana fuskantar kalubalen tsaro da ayukan 'yan bindiga masu kai hare-hare, satar shanu da kuma satar jama'a domin karbar kudin fansa.

Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle
Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle

To sai dai gwamnan jihar Bello Muhammad Matawalle ya ce yana samun nasara a shirin sulhu da yake yi da 'yan ta da kayar baya a jihar, duk da yake masu lura da fashin baki na bayyana ra'ayin cewa har kawo yanzu shirin sulhun bai yi wani tasiri ba, la'akari da ci gaba da ayukan na 'yan bindiga a jihar.

XS
SM
MD
LG