Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fursunoni 6 Cikin Wadanda Suka Gudu Daga Gidan Yarin Imo Sun Mika Kansu


Gidan Yarin Owerri.
Gidan Yarin Owerri.

Hukumar da ke kula da gidan yarin jihar Imo ta ce fursunoni shida sun dawo bisa radin kansu yayin da wasu 35 suka ki tserewa daga inda aka tsare su bayan da aka kai hari a gidan yarin ranar Litinin a garin Owerri.

Mukaddashin babban kwanturola-Janar na Hukumar kula da gaggawa ta Najeriya NCoS, John Mrabure, shi ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa.

A cewar sanarwar, Mrabure ya bayar da umarnin a gudanar da cikakken bincike a kan lamarin.

Wani mai magana da yawun kungiyar ‘yan asalin yankin Biafra masu neman ballewa ya shaida wa kamfanin dillacin labarai na AFP cewa, zargin da ake yi kungiyar cewa ita ke da alhakin harin ba shi da kanshin gaskiya.

Karin bayani akan: Boko Haram, Owerri​, John Mrabure, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.

Jihar Imo ta dade tana a matsayin wurin da kungiyoyin 'yan awaren ke tinkaho da shi, yayin da dangantaka tsakanin gwamnatin tsakiya da' yan asalin kabilar Ibo ta yi tsami.

Da yake maida martani dangane da lamarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya umarci dukkanin hukumomin tsaro da na leken asiri su tabbatar da kame tare da hukunta duk wadanda suka kai munanan hare-hare a shalkwatar rundunar ‘yan sanda ta jihar Imo da kuma gidan yarin na Owerri da safiyar Litinin.

Zaben 2023

TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Tasirin Da Zaben Donald Trump Zai Yi A Harkokin Kasashen Duniya.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:50 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG