Kwamishinan tsaron cikin gida Samuel Aruwan ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a cewar rahotanni.
Sanarwar ta ce da tsakar ranar Litinin rundunar sojin Najeriya ta ce ta kubutar da biyar daga cikin daliban kwalejin.
“Sojoji sun sanar da gwamnatin jihar Kaduna cewa, biyar daga cikin daliban kwalejin da aka sace sun kubuta, suna nan can a wani asibitin sojoji ana duba lafiyarsu.” Gidan talbijin na Channels TV ya ruwaito sanarwar mai dauke da sa hannun Aruwan tana cewa.
“Gwamnatin jihar Kaduna, za ta ci gaba da fitar da bayanai kan wannan al’amari.” In jaridar The Nation wacce ta ruwaito sanarwar.
A ranar 12 ga watan Maris aka sace daliban, bayan da wasu ‘yan bindiga suka kai wani hari a makarantarsu da ke Afaka.
Da farko maharan sun kaikaici kwashe daliban da yawansu ya haura 100 amma wani artabu da ‘yan bindigar suka yi da sojoji ya sa suka kare da dalibai 39.
Ita dai gwmanatin jihar Kaduna ta ce ba ta da shirin yin sulhu da ‘yan bindiga kuma ba za ta biya kudin fansa ba, abin da ya sa wasu ke ganin aka jima ba a karbo daliban ba.
Arewa maso yammacin Najeriya na fama da matsalar satar mutane don neman kudin fansa, wacce ake dora alhakin hakan akan Fulani da ke daji.