Ukraine Ta Kai Wa Rasha Mummunan Hari

Russia-Ukraine

Ukraine ta kai wani babban hari a birnin Moscow a ranar Laraba tare da harbo jiragen sama mara matuka guda 11 da jami'an tsaron kasar Rasha suka ce na daya daga cikin hare-hare mafi girma na jirage marasa matuka akan babban birnin kasar tun bayan yakin na Ukraine da aka fara a watan Fabrairun 2022.

Mayakan Ukraine masu aiki kan jirage marasa matukai

Yakin, wanda ake yi akasari da makaman atilare da jirage marasa matuka a dazuzzuka da kauyukan gabashin Ukraine, ya yi kamari a ranar 6 ga watan Agusta lokacin da Ukraine ta tura dubban sojoji zuwa yankin Kursk na yammacin Rasha.

Har ila yau, cikin tsawon watanni, Ukraine ta yi yakin da ke kara yin barna a kan matatun mai da filayen jiragen sama akan Rasha wacce ita ce ta biyu a duniya wajen fitar da mai, ko da yake manyan hare-haren jiragen sama marasa matuka a yankin Moscow da ke da fiye da miliyan 21 ba su da yawa.

Russia

Ma'aikatar tsaron Rasha ta ce ta lalata jimillar jirage mara matuka 45 a kan yankinta, wadanda suka hada da 11 a yankin Moscow, 23 a kan iyakar Bryansk, 6 a yankin Belgorod, uku a yankin Kaluga, biyu kuma a yankin Kursk.

-Reuters