Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelenskyy ya jaddada muhimmancin yaki domin kare birnin Bakhmut da ke gabashin kasar, yana mai shaidawa kamfanin dillancin labarai na Associated Press a jiya Talata cewa, galaba kan Ukraine a can, zai haifar da matsin lamba daga alummar kasa-da-kasa da wasu a cikin Ukraine su sasanta da Rasha.
Zelenskyy ya ce Ukraine ba zata shiga duk wata tattaunawar zaman lafiya da Rasha ba, har sai dakarun kasar ta Rasha sun fice baki daya daga dukan yankin kasar Ukraine.
Tun lokacin da Rashar ta kaddamar da cikakkiyar mamayar tata a shekarar da ta gabata, ta yi ikirarin mamaye yankuna 4 na Ukraine, a wani yunkuri da baki dayan babban taron Majalisar Dinkin Duniya MDD yayi Allah wadai da shi a zaman ya saba doka.
Kasashen yammaci na ganin cewa rashin wani babban muhimmanci ga Bakhmut, suna cewa don Ukraine ta rasa wajen, ba zai yi wani babban tasiri ba ga daukacin yakin.
Sai dai Zelenskyy ya fadawa kamfanin na AP cewa, ko wane sashe na yakin yana da muhimmanci.