Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ukraine Ta Kai Kazamin Hari Kan Yankunan Iyaka Na Rasha


Dakarun Ukraine sun kai farmaki a yankunan kan iyakar da safiyar Talata, a wani hari da ya kasance mafi girma da samun nasara da Kyiv kai a cikin shekaru 2 da rabi na yakin.

Rasha ta fada jiya Assabar cewa ta kwashe dubban mutane daga yankin kan iyakarta, tare da kaddamar da farmakin yaki da ta'addanci, a daidai lokacin da take kokarin shawo kan wani babban kutse na Ukraine.

A lokaci daya kuma, Moscow ta yi gargadin cewa fadan da ake gwabzawa a yankin Kursk da ke yammacin kasar Rasha na yin barazana ga wata tashar makamashin nukiliya.

Dakarun Ukraine sun kai farmaki a yankunan kan iyakar da safiyar Talata, a wani hari da ya kasance mafi girma da samun nasara da Kyiv kai a cikin shekaru 2 da rabi na yakin.

Dakarun ta sun dada matsawa gaba da tazarar kilomita da dama, lamarin da ya tilastawa sojojin Rasha yin gaggawar waiwayar wurin ajiyar makamai da karin kayan aiki, ko da yake babu wani bangare da ya ba da cikakken bayani kan adadin sojojin da aka sanya.

Russia Ukaraine
Russia Ukaraine

Jami’an yankin sun yi cikakken bayani kan yadda fararen hula da sika fice daga garuruwa da kauyukan da ke kusa da yankin da ake gwabzawa.

Sama da mutane 76,000 ne aka kwashe su na wucin gadi zuwa wasu wuraren tudun mun tsira," kamar yadda kamfanin dillancin labarai na gwamnati TASS, ya ruwaito wani jami'in ma'aikatar kula da ayukan gaggawa na yankin yana fada a wani taron manema labarai a jiya Asabar.

An kai agajin gaggawa zuwa yankin kan iyaka, an kuma sanya karin jiragen kasa zuwa babban birnin kasar, Moscow, ga mutanen da suka arce wa yakin.

Amma da yammacin jiya Asabar din, an yi ta harbe-harbe ta sama a Kyiv, babban birnin kasar Ukraine.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG