“Ina mai farin cikin shaida cewa tsohon darakta a hukumar kula da shige da fice da yaki da fasakwabri, kuma jigo a harkar kula da kan iyakoki, Tom Homan, zai shigo cikin gwamnatin Trump, a matsayin mai kula da kan iyakokin kasarmu”, ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na “Truth Social”.
“Na san Tom da jimawa, kuma babu wanda ya fi shi a harkar sa idanu da kula da kan iyakokinmu.”
Trump ya bayyana cewa Homan zai kula da harkar “tasa keyar bakin haure zuwa kasashensu na asali”.
Dan jam’iyyar Republican mai shekaru 78 ya sha alwashin kaddamar da aikin tasa keyar bakin haure mafi girma a tarihin Amurka-a ranar farko ta hawansa kan karagar mulki.
Ya yi ta nanata kyamarsa game da yin kaura ta baranauniyar hanya yayin yakin neman zabensa, inda ya rika amfani da kausasan kalamai akan mutanen da suka “gurbata jinin” Amurka.
-Reuters