Trump Ya Sha Alwashin Yin Amfani Da Sojoji Wajen Korar Bakin Haure Marasa Takardu

Zababben shugaban kasar Amurka Donald Trump lokacin wani taro na manema labarai a birnin New York.

Zababben Shugaban Amurka Donald Trump ya sha alwashin yin amfani da sojojin kasar wajen tasa keyar miliyoyin bakin hauren dake zaune a kasar ba tare da cikakkun takardu ba, shirin da ya sabawa al’adar Amurka ta yin amfani da sojoji a cikin gida

Sai dai masana shari’a na ganin zai yi wuya a iya kalubalantarta a kotu.

Mashawartan trump sun ce suna da niyar yin amfani da sojoji wajen gina wuraren tsare bakin hauren da basu da takardun zama ko kuma yin safararsu zuwa wajen Amurka, abin da zai baiwa jami’an tsaron kan iyaka da na kula da shige da fice kariya daga tuhuma ko tsarewa.

Kamun bakin haure a kan iyakar Amurka

Masana na cewa gwamnati na da kariyar doka idan ta takaita rawar da sojojin za su taka zuwa na tallafawa, musamman a kan iyakar Amurka da Mexico, ba tare da sunyi mu’amala da wadanda ake tuhuma ba.

“Ina ganin hakan ba zai fuskanci kalubalen da zai yi nasara ba,” a cewar Ryan Burke, farfesa akan al’amuran da suka shafi aikin soja da dabarun yaki a kwalejin sojin saman Amurka, a jawabinsa na kashin kansa.

“Akwai boyayyun abubuwa da dama a cikin wadannan dokoki da basu fito karara sun ce, kai ba zaka iya aikata haka ba kai tsaye.”

Dokar tabbatar da tsaron al’umma ta 1878 (Posse Comitatus) ta haramta yin amfani da sojojin tarayya wajen aiwatar da doka a cikin kasa.

U.S. Capitol a Washington, D.C.

Majalisa ta yi togaciyar da ta sahalewa shugabannin kasa yin amfani da sojoji wajen tallafawa al’amura irin su yaki da haramtaccen fataucin miyagun kwayoyi da kuma lokutan tarzoma.

-Reuters