Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Me Zai Faru Da Shari'un Da Ke Kan Trump Yanzu Da Ya Zama Zababben Shugaban Kasa?


Donald Trump
Donald Trump

Har yanzu babu tabbacin ko za a yanke hukumci kan shari'un da ke gaban kotu inda ake tuhumar zababben Shugaban kasar Amurka da aikata wadansu laifuka.

A watan Mayun da ya wuce ne aka samu tsohon Shugaban Amurka Donald Trump da aikata laifuka 34 akan abinda ya shafi ba da bayanan da ba na gaskiya ba game da harkokin kasuwancinsa don kawar da wasu munanan bayanai game da shi gabanin zaben 2016 da ya lashe. An jinkirta yanke masa hukunci har sai bayan zaben bana, amma yanzu da ya zama zababben Shugaban kasa, ba a san abinda zai biyo baya ba.

Shin ko za a yanke wa Shugaban kasa mai jiran gado, Donald Trump hukunci kan laifukan da aka same shi da su?

Wannan wata tambaya ce da har yanzu ba a san amsarta ba, yayin da alkalin jihar New York Juan Merchan ya duba irin yanayin shari'ar da ba a taba gani ba, inda wani tsohon Shugaban Amurka wanda aka samu da laifi kuma shi ne ya zama zababben shugaban kasa.

A watan Mayu, aka samu Trump da aikata laifuka 34 akan ba da bayanan da ba na gaskiya ba game da harkokin kasuwancinsa don yin rufa-rufa kan biyan kudin toshiyar baki ga wata tauraruwar fina-finan batsa mai suna Stormy Daniels don dakile wata badakalar lalata gabanin ya lashe zabe a 2016.

An jinkirta yanke wa Trump hukunci akan shari'ar toshiyar bakin lokuta da yawa, kuma nasarar da ya samu a zaben da aka yi a farkon watan Nuwamban bana ta kara kawo shakku kan shari’ar.

A hirar ta da Muryar Amurka, Anna Cominsky ta sashen koyar da aiki lauya a jami'ar birnin New York ta bayyana cewa, "Hakika, babban abin dubawa a nan shine ko za a yanke wa Trump hukunci. Kuma hakan ya hada da ko yanke hukuncin zai faru kafin ya hau mulki, ko sai bayan ya hau mulki, ko kuma kawai za a yi watsi da shari'ar.”

Tawagar lauyoyin da ke kare Trump na jayayya da cewa wani babban hukunci da kotun kolin kasar ta yanke a watan Yuli ta ba shi kariyar shugaban kasa kuma ya kamata a yi watsi da karar gaba daya.

Sai dai lauyan gundumar Manhattan Alvin Bragg, ya ce masu taimaka wa alkali yanke hukunci sun riga sun yanke hukunci kan lallai ya aikata laifin kafin kotun kolin ta yanke nata hukuncin, kuma Trump ba Shugaban kasa bane a lokacin.

A wata wasika da ya tura wa alkalin kotun, ya nuna cewa, masu gabatar da kara ba zasu amince da duk wani yunkuri na neman yin watsi da shari'ar ba, amma a shirye suke su jinkirta yanke hukunci har sai bayan wa'adin Trump.

"Idan Juan Marshan ya ce ya yarda da shawarar da masu gabatar da karar suka gabatar a matsayin abu mai yiwuwa, to zai fara aiki akan abin da ake kira "dakatar da ko jinkirta shari'ar" bisa la'akari da yanayin da ba a saba gani ba, inda wanda ake tuhuma ya zama Shugaban kasar Amurka, kuma zai dakatar da shari'ar har zuwa 2029, bayan Donald Trump ya sauka daga mulki."

Shari'ar biyan kudin toshiyar baki ba ita ce kadai abin da zababben Shugaban zai fuskanta ba.

Akwai kararraki biyu na tarayya da mai gabatar da kara na musamman Jack Smith ya gabatar, daya ana zargin Trump da yin sakaci da wasu takardu na sirri, sai kuma yin katsalandan a zabe, wanda rahotanni suka ce ana gab da yanke hukunci a kansu, yayin da wata manufa ta Ma'aikatar Shari'ar kasar ta ce ba za a hukunta wani shugaba da ke kan Mulki ba.

Ko da yake, shari'ar yin katsalandan a zabe a jihar Georgia ba ta fada a karkashin wannan tanadin dokar ta tarayya ba.

"A zahiri, jihar Georgia tana da 'hurumin ci gaba da shari'arta ba tare da manufar hukumar shari'ar ta taka mata burki ba. Amma za ta iya yin hakan? Ko akwai, shin ma zai yiwuwa a sa ran jihar zata iya ci gaba da shari'ar, kuma a sa ran za a sami hadin gwiwar Donald Trump, wanda hakan zai bukaci hadin gwiwar Fadar White House don ci gaba da shari'ar yayin da wanda ake tuhuma ke aiki a matsayin shugaban Amurka?"

Yanayin abubuwan da ba a taba fuskanta ba yanzu sun haifar da sabon yanayin shari'a.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG