Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zan Kara Harajin Kashi 25% Kan Kayan Mexico,Canada, Kashi 100 Kan Na China-Trump


 Donald Trump
Donald Trump

Zababben Shugaban Amurka Donald Trump ya fada a ranar Litinin cewa, a ranar farko da ya hau kan karagar mulki, zai sanya harajin kashi 25% kan duk kayayyakin da ake samu daga Mexico da Canada, da kuma karin harajin kashi 10 cikin 100 kan hajoji daga China.

Trump ya yi nuni da damuwar da ke tattare da shige da fice ba bisa ka’ida ba, da cinikayyar haramtattun kwayoyi.

"A ranar 20 ga watan Janairu, a matsayin daya daga cikin umarni na farko da zan zartar, zan sanya hannu kan duk wasu takaddun da suka wajaba don cajin Mexico da Canada harajin kashi 25% kan duk kayayyakin da ke shigowa Amurka ta budaddun iyakoinsu marasa ma'ana," in ji Trump a dandalin sada zumuntarshi "Truth Social".

Trump ya ce harajin zai ci gaba da aiki har sai kasashen biyu sun dakile safarar miyagunkwayoyi musamman fentanyl da bakin haure da ke tsallakawa kan iyaka ba bisa ka'ida ba ke safara. Dangane da kasar Sin, zababben Shugaban kasar ya zargi Beijing da rashin daukar kwararan matakan dakile kwararar haramtattun kwayoyi da ke tsallaka kan iyakar Amurka daga Mexico.

"Za mu kara wa kasar Sin karin harajin kashi 10%, fiye da duk wani karin haraji, kan dukkan kayayyakinsu da ke shigowa Amurka, har zuwa lokacin da suka daina" in ji Trump.

A baya dai Trump ya yi alkawarin kawo karshen matsayin kasuwancin da kasar Sin ta fi samun tagomashi tare da dora haraji kan kayayyakin da China ke shigowa da su da kashi 60 cikin 100 - wanda ya zarce na wanda aka sanya a wa'adinsa na farko.

Tattalin arzikin kasar Sin yana cikin wani yanayi mai matukar rauni idan aka yi la'akari da durkushewar kadarorin kasar da aka dade ana fama da shi, da hadarin bashi da kuma karancin bukatun cikin gida. Darajar Dalar Amurka ta cira da sama da 2% akan peso na Mexico MXN = bayan da Trump ya wallafa matsayarsa a dandalin sada zumunta.

Ma'aikatar harkokin wajen Mexico da ma'aikatar tattalin arzikin kasar ba su yi wani bayani kai tsaye ba lokacin da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya tuntube su.

Nan take ofishin jakadancin China da ke Washington, da ofishin Firayim Ministan Kanada Justin Trudeau. da ma’aikatar harkokin wajen Canada ba su amsa bukatun daban-daban da kamfani dillacin labaran ya gabatar ba na yin sharhi.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG