Zababben shugaban Amurka Donald Trump ya zabi Scott Turner, tsohon dan wasan kwallo wanda ya taba rike mukami a fadar white House a lokacin shugabancin Trump na farko, da ya jagoranci bangaren gidaje da raya birane.
Turner, mai shekaru 52 a duniya, shine bakar fata na farko da aka zaba da zai kasance mamba a majalisar gwamnatin ta Republican.
Turner ya taso ne a Richardson da ke yankin Dallas, ya kuma yi karatun sa a jami’ar Illinoi Urbana-Champaign. Shahararren dan wasa ne da ya kasance mai tsaron baya a NFL da ya shafe kakar wasanni tara da ya fara tun a shekarar 1995, inda ya bugama kungiyoyin Washington Redskins, San Diego Chargers da Denver Broncos wasanni.
A lokutta dabam dabam yayi aiki na wucin gadi da dan majalisar wakilai Duncan Hunter, inda a shekarar 2004 ya cigaba da aiki gadangadan da dan majalisar wakilan.
Hakazalika Turner yayi aiki da wani kamfanin komputa inda ya rike matsayin ‘Chief inspiration officer’ a turance, inda ya taka gagarumar rawa a fannoni dabam dabam. Sannan kuma gwani ne wajen iya magana.
Shi da medakin shi Robin Tuner, sun samar da wani Shirin da ba na neman riba ba, na inganta ilmin yara kanana. Cocin shi na Prestonwood Baptist ya sa shi cikin jerin pastocin dake wa’azi lokaci lokaci a cocin. Ya kasance shugaba a cibiyar samar da damar samun ilmi ta American First Policy, wata gagarumar cibiya da tsofaffin ma’aikatan gwamnatin Trump ta samar da nufin soma aiki kafin dawowar shi a karo na biyu.
Trump ya gabatar da Turner a watan Apirilun shekarar 2019 a matsayin shugaban sabuwar majalisar farfado da damarmaki na fadar white House. Trump ya dagawa Turner tuta sakamakon gagarumar rawar da ya taka a kokarin sauya rayuwar al’ummomi da dama da aka zalunta.
Dandalin Mu Tattauna