ABUJA, NIGERIA - Babban daraktan kamfen din, Gwamna Simon Lalong na Jihar Filato, ya fitar da jadawalin kamfen din da zai kammala kwana 10 gabanin ranar zabe a ranar 25 ga watan Fabrairun badi.
Cikin kamfen din akwai zuwa Lagos da Kano sau biyu don girman jihohin ko muhimmancinsu a siyasance ga dan takaran na APC.
Hakanan kamfen din na Tinubu ya tsara zuwa wasu jihohin kudu maso gabas a ranakun Litinin da haramtacciyar kungiyar ‘yan awaren Biyafara, IPOB ta ayyana cewa kar kowa ya rika fitowa a ranakun; da hakan ya zama matsa lamba kan gwamnatin taraiya ta sako shugaban su Nnamdi Kanu da ke fuskantar shari’ar cin amanar kasa da ta’addanci.
Yayin da tuni dan takarar jam’iyyar LEBA Peter Obi ke cewa zai tattauna da duk masu korafi irin ‘yan awaren na Biyafara, Tinubu bai bayyana matsayinsa a kan kungiyar ba.
A zantawar sa da gidan talabijin na CHANNELS, Obi ya ce bai amince da ayyana ‘yan awaren da cewa ‘yan ta’adda ne kamar yadda gwamnati ta ayyana ba. Obi na da ra’ayin matukar a ka takura mutum zai iya aikata komai don haka ya na rayuwa ne a garin Anacha kuma ya na hulda da ‘yan awaren da ba ya ganin ‘yan ta’adda ne.
‘Yar siyasa daga arewa maso gabas Talatu Fara ta ce burin masu kada kuri’a a yi zabe lafiya ta na mai kira ga mata su fito su zabi duk wanda su ke so duk da ita APC ta ke yi.
Game da barayin daji, shi ma ‘dan takarar NNPP Rabi’u Musa Kwankwaso na ganin tattaunawa da su don dawo da su kan hanya shi ne mafi a’ala kuma haka ya ke da muradi in ya lashe zabe.
A fili ya ke cewa kamar yadda a 2015 batun ‘yan Boko Haram ne ya mamaye lamuran kamfen, wanann babban zabe na 2023 zai duba hanyoyin kawo karshen ‘yan awaren Biyafara, masu neman kafa kasar Odudua da kuma ‘yan bindiga da ke sace mutane musamman a arewa maso yamma.
Saurari cikakken rahoto daga Nasiru Adamu El-hikaya:
Your browser doesn’t support HTML5