Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tinubu, Atiku, da Peter Obi Sun Jajantawa Davido Kan Mutuwar Dansa


Davido yana waka a Abidjan, Ivory Coast, Aug. 30, 2019.
Davido yana waka a Abidjan, Ivory Coast, Aug. 30, 2019.

‘Yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, da na PDP, Alhaji Atiku Abubakar, da kuma Labour Party, Mista Peter Obi, duk sun jajanta wa mawakin nan na Afrobeat na Najeriya, Davido, da matarsa Chioma, bisa rashin dansu, Ifeanyi Adeleke.

Rasuwar Ifeanyi wanda kwanan nan ya cika shekaru 3 a duniya a ranar 20 ga watan Oktoba ta zo da mamaki ga daukacin al'ummar kasar. An tabbatar da mutuawar Ifeanyi ne bayan nutsewar ruwa a wurin wasan nikayya da ke cikin gidan mahaifinsa a Legas.

'Yan takarar sun shiga jerin ‘yan Najeriya da dama da suka mika sakon ta’aziyya zuwa ga Davido da matarsa Chioma, inda suke yi masu addu’ar Allah ya baiwa Iyalan Adeleke ikon jure wannan babban rashi na dansu.

Da yake magana a shafinsa na Twitter, Peter Obi ya wallafa cewa, “Ina mika sakon ta’aziyyata ga Davido da Chioma, bisa rasuwar dansu Ifeanyi. Ba zan iya fara tunanin bakin cikin da suke ciki a halin yanzu ba. Allah Ya kara masu hakuri da dangana a wannan mawuyacin lokaci."

Shima da yake mika sakon ta'aziyya ga iyalan Adeleke, mai Magana na yawun kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyar APC, Festus Kenyamo, SAN, ya yi ta'aziyyar marigayi Ifeanyi a shafinsa na Twitter.

Ya rubuta, “A gaskiya ina jiran bayanin iyali kan wannan batun don in tabbata. Ina mika ta'aziyyata ga iyalin wannan matashin da suka fuskanci wannan bakin ciki a wannan lokaci. Allah Madaukakin Sarki ya baiwa Iyalan Adeleke kwarin guiwar jure wannan rashin da ba za a iya maye gurbinsa ba; da kuma duk wadanda suka fuskanci irin wannan halin”.

XS
SM
MD
LG