Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinuba ya rattaba hannu kan dokar da ta amince da naira 70,000 a matsayin albashi mafi karanci a kasar.
A makon da ya gabata Majalisar Dokokin kasar ta amince da kudurin dokar wanda za a rika biya a matsayin albashi mafi karanci a kowane wata.
Tinubu ya sanya hannu a kan dokar ne a Fadar gwamnati da ke Abuja a ranar Litinin a lokacin taron majalisar zartawa da ake yi a kowane mako.
Shugaban Majalisar Dattawa Godswin Akpabio ya jagoranci tawagar ‘yan majalisar dokoki a lokacin sanya hannu a wannan sabuwar dokar.
Gabanin amincewa da wannan kudurin doka, an yi ta kai ruwa rana tsakanin kungiyar kwadago da gwamnati kan albashin.