Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

SGF, NSA Da Ministocin Najeriya Sun Shiga Taron Gaggawa Kan Zanga-zangar Tsadar Rayuwa


Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu (Hoto: Facebook/Bola Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu (Hoto: Facebook/Bola Tinubu

Zanga-zangar tsadar rayuwa da aka shirya gudanarwa a watan Agusta na kara daukar hankali a shafukan sada zumunta.

A yau Laraba Sakataren gwamnatin tarayya, George Akume, ya gana da ministocin kasar a kan zanga-zangar adawa da matsalar tattalin arziki da matasan Najeriya ke shirin yi a fadin kasar.

Ganawar sirrin ta samu halartan sama da ministoci 40 daga majalisar ministocin kasar.

Wasu daga cikin Ministocin da aka gansu sun hada da Nyesom Wike (FCT), Yusuf Tuggar (Ma’aikatar Harkokin Waje), Zephaniah Jisalo (Ayyuka na Musamman), Tahir Mamman (Ilimi), da Abubakar Bagudu (Kasafin kudi da tsare-tsare).

Sauran sun hada da Wale Edun (Kudi), Mohammed Idris (Yada Labarai), Bello Matawalle (Tsaro), David Umahi (Ayyuka), da kuma mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA) Nuhu Ribadu, da dai sauransu.

A halin da ake ciki kuma, shugaba Bola Tinubu a ranar Talata ya roki ‘yan Najeriya da su jingine Shirin zangar-zangar tsadar rayuwa mai taken ‘EndBadGovernance’ da aka shirya gudanarwa wata mai zuwa.

An shirya gudanar da zanga-zangar nuna adawa da matsalar tattalin arziki da ke kara daukar hankali a shafukan sada zumunta, a duk fadin jihohin Najeriya da kuma babban birnin tarayya Abuja a cikin watan Agusta.

Sai dai har yanzu ba a bankado wadanda suke shirya zanga-zangar ba.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG