Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Malisar Dattawa ta Zartar Da Kudirin Dokar Mafi Karancin Albashi


Zauren majalisar dattawan Najeriya (Facebook/Nigerian Senate)
Zauren majalisar dattawan Najeriya (Facebook/Nigerian Senate)

Majalisar ta amince da dokar ne ranar Talata bayan da Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya aika kudirin doka kan sabon mafi karancin albashin ma’aikata na kasa zuwa Majalisar domin amincewa da shi.

Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da kudirin dokar kara mafi karancin albashi zuwa naira 70,000.

Majalisar dattawan ta zartar da kudirin, wanda ya tsallake karatu na 2 dana 3, ‘yan mintuna kadan bayan da Shugaban kasa Bola Tinubu ya aiko da shi.

A wata kuri’ar da kowa ya amince da ita bayan da babban kwamitin majalisar ya kammala nazarin akansa, kudirin mafi karancin albashi ya tsallake karatu na 3 kuma aka zartar dashi zuwa doka.

Da safiyar yau Talata, shugaban Najeriya ya aike da kudirin mafi karancin albashin ga majalisar kasa domin yin nazari tare da zartar da shi.

Majalisun Dattawa dana Wakilai inda ya bukaci gaggauta nazarin kudirin gyaran dokar mafi karancin albashin kasa na 2019 domin kara albashin daga Naira dubu 30 zuwa dubu 70.

A ranar alhamis din da ta gabata ne kungiyoyin kwadago na Najeriya suka amince da sabon mafi karancin albashi na Naira 70,000 a wata bayan tattaunawa da gwamnatin kasar, lamarin da ya kawo karshen kiki-kakan da aka samu tsawon watanni da kuma barazanar yin yajin aikin.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG