Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Najeriya Da Kungiyar Kwadago Sun Amince Da Naira 70,000 A Matsayin Mafi Karancin Albashi


Shugaba Bola Tinubu
Shugaba Bola Tinubu

A jiya Alhamis kungiyoyin kwadago na Najeriya suka amince da sabon mafi karancin albashi na Naira 70,000 a wata bayan tattaunawa da gwamnatin kasar, lamarin da ya kawo karshen kiki-kakan da aka samu tsawon watanni da kuma barazanar yin yajin aikin.

Kasar, wacce ta fi yawan al'umma a nahiyar Afirka dai na fama da matsalar tsadar rayuwa da ba a ga irinta ba cikin shekaru da yawa, lamarin da ya kawo fargabar yiwuwar barkewar zanga-zangar gama-gari kamar yadda aka yi a kasar Kenya, wacce ta girgiza kasar kusan tsawon wata guda.

Manyan kungiyoyin kwadagon Najeriya guda biyu, na Nigerian Labour Congress da Trade Union Congress, sun kafe kan cewa tashin farashin kayayyaki da faduwar darajar naira sakamakon sauye-sauyen da shugaba Bola Tinubu ya yi na shafar ma'aikata sosai.

Hauhawar farashin kayayyaki na lakume kudaden shiga da ake samu tare da shafar miliyoyin 'yan Najeriya da ke fafutukar biyan bukatunsu na yau da kullun.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG