Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya aika kudirin doka kan sabon mafi karancin albashin ma’aikata na kasa zuwa majalisar dokokin kasar domin amincewa da shi.
A ranar alhamis din da ta gabata ne kungiyoyin kwadago na Najeriya suka amince da sabon mafi karancin albashi na Naira 70,000 a wata bayan tattaunawa da gwamnatin kasar, lamarin da ya kawo karshen kiki-kakan da aka samu tsawon watanni da kuma barazanar yin yajin aikin.
Da yake jawabinsa na na ranar Dimokradiyyar bana Shugaba Tinubu ya tabbatar wa kungiyar kwadagon kasar cewa nan ba da jimawa ba za a aika da kudirin doka kan sabon mafi karancin albashin ma’aikata na kasa zuwa majalisar dokokin kasar domin amincewa da shi.
Kasar, wacce ta fi yawan al'umma a nahiyar Afirka dai na fama da matsalar tsadar rayuwa da ba a ga irinta ba cikin shekaru da yawa, lamarin da ya kawo fargabar yiwuwar barkewar zanga-zangar gama-gari kamar yadda aka yi a kasar Kenya, wacce ta girgiza kasar kusan tsawon wata guda.
Manyan kungiyoyin kwadagon Najeriya guda biyu, na Nigerian Labour Congress da Trade Union Congress, sun kafe kan cewa tashin farashin kayayyaki da faduwar darajar naira sakamakon sauye-sauyen da shugaba Bola Tinubu ya yi na shafar ma'aikata sosai.
Dandalin Mu Tattauna