Ministan Yada Labarai Muhammad Idris, yace gwamnatin tarayya da shugabannin hadaddiyar kungiyar kwadago sun amince da naira dubu 70 a matsayin mafi karancin albashin ma’aikatan Najeriya.
“A yau Alhamis muna farin cikin sanar da cewa hadaddiyar kungiyar kwadago da gwamnatin tarayya sun amince da yin kari akan mafi karancin albashi na naira dubu 62. Don haka sabon mafi karancin albashin da ake sa ran mai girma shugaban kasa ya gabatarwa majalisar kasa shine naira dubu 70, “a cewar Muhammad Idris.
Yayin bada sanarwar ga manema labaran fadar shugaban kasa, an ga shugaban kungiyar kwadago ta NLC, Joe Ajaero da takwaransa na tuc, Festus Osifo tare da Ministar Kwadago, Nkiruka Onyejeocha da sauran jami’an gwamnati a kewaye da ministan.
Dandalin Mu Tattauna