Mahalarta taron kasa da kasa akan makiyaya da manoma na cigaba da bayyana hanyoyin kawo karshen tashin tashina tsakanin bangarorin biyu.
Barrister Solomon Dalung na cikin mahalartar taron. Yace ganin irin tashin hankalin dake barkewa tsakanin makiyaya da manoma da kuma irin abun da wasu 'yan tsageru ke yi da bindigogi yasa gwamnatin tarayya ta tarasu domin samo bakin zaren da zai kai ga sulhu. Yace akwai kyakyawar dangantaka tsakanin makiyaya da masu daukan makamai domin dukansu suna daji ne. Bafullatani na ganin wanda ya sameshi a daji da'uwansa ne. Yayin da bafillatani ke kukan ba'a kula da shi ba shi kuma mai dauke da bindiga yana cewa an yi masa rashin gaskiya.
Idan ba'a samu kyakyawar fahimta ba idan Bafillatani da Dan bindiga sun hada baki to al'umma tana cikin wahala. Taron ka iya taimaka inganta harkokin tsaro domin ba'a taba yin irinsa ba. Taron ya nuna an kama hanyar yadda za'a magance barkewar tashin tashina. Taron nada kyakyawar manufa.
Shugaban kungiyar al'ummar kudancin Kaduna Dr. Ephraim Goje yace taron zai taimaka. Yace yarjejeniyar da suka yi da makiyaya zata samu karfin gwiwa yanzu. Yana ganin idan aka cigaba da hakan za'a samu dawamanmen zaman lafiya. Yace sun goyi bayan irin wannan taron. Yana fata zasu cigaba da tattaunawa.
Wasu makiyaya da suka bada tasu gudunmawar sun ce akwai wasu abubuwa da yakamata gwamnati ta duba. Sun ce a wurinsu jeji ya kare kuma babu burtuli. Yace abun dake hada manoma da makiyaya shi ne idan sun tafi kiwo lokacin damuna kuma sun dawo da kaka kamata yayi manoma su saki gonakansu shanu su yi kiwo amma sai su ki kare aikin gona. Na biyu an kashe burtuli duka. Wurin tafkin ruwa duk an sare. Abu na uku bafillatani baya samun kulawa daga gwamnati idan wani bala'i ya samu shanunsa. Mutuwar saniya daya ka iya kawowa bafillatani rudu, ya kidime. Idan gwamnati ta tallafa masa hankalinsa zai kwanta.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5