Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabon Rikicin Yankin Wukari Ya Haddasa Asarar Rayuka Da Dukiyoyi


Wuraren da aka kai hare-hare
Wuraren da aka kai hare-hare

Duk da yarjejeniyar zaman lafiya da ake ikirarin cimma tsakanin Fulani da Hausawa da Jukunawa sabon rikicin da ya sake barkewa a yankin Wukari ya haddasa asarar rayuka.

Wasu rahotanni dake fitowa daga yankin Wukari inda aka sake samun barkewar rikici suna karo da juna.

Kodayake an kara tura karin sojoji da 'yansandan kwantar da tarzoma a yankin Wukarin dake kudancin jihar Taraba rahotanni na cewa adadin wadanda suka rasa rayukansu na karuwa.

Wasu mazauna garin da suka tsira da rayukansu sun ce adadin wadanda aka kashe sun fi ashirin wasu da dama kuma sun jikata. Wani yace an kusan kone rabin garin gefen Hausawa. Wani ma cewa yayi an kashe mutane sama da dari kodayake babu wani tabbaci.

Yayin da mutane ke cewa sun ga gawarwaki fiye da ashirin ita kuwa rundunar 'yansandan jihar Taraba tace mutane hudu aka kashe. Kuma kawo yanzu babu wanda aka kama. ASP Kwaje kakakin runudunar yace suna nan suna sintiri ciki da wajen Wukari. Ya tabbatar da ganin gawarwaki hudu kawai.

Daniel Ishaya Gani mai wakiltar mazabar Wukari a majalisar dokokin jihar yace suna kokarin su hada kawunan al'ummominsu wato da Musulmai da Kiristoci da Fulani da Jukun da Hausawa da Tiv domin su bayyana damuwarsu. Yace dole ne su zauna da juna cikin lumana.

To amma yayin da suke kokarin shawo kan mutane, Ishaya gani yace wasu bata gari basa son a zauna lafiya domin idan an zauna lafiya ba zasu cimma burinsu ba, kamar sace-sace da suke yi.

Shugaban kungiyar matasan Jukun Sabo Wukari yace yana ganin wasu ne ke son mayar da hannun agogo baya a kokarin da a keyi na wanzar da zaman lafiya. Yace idan ba haka ba yaya za'a ce sarkin Wukari ya hada Musulmai da Kirista a fadarsa ya sa sun fahimci juna kuma sun yi alkawarin zaman lafiya kana kuma rikici ya barke kwana daya da yin taron. Yace taron ya sa suna ganin rikici ya wuce amma kwatsam sai gashi kuma wani sabon ya faru wanshekare. Yace abun ya basu mamaki.

Ga rahoton Ibrahim Abduaziz.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:13 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG