Harin da aka kai daren shekaran jiya yayi sanadiyar mutuwar mutane takwas. Kakakin rundunar tsaron Keften Ikediachi Iweha ya shaidawa wakiliyar Muryar Amurka cewa maharan sun kai hari ne a kauyukan Jol da Rim da Baci.
Kakakin yace an rasa rayuka takwas, fararen hula biyar da jami'an tsaro uku. Jami'an dake wurin yace sun yi iyakacin kokarinsu, sun kwashi lokaci suna fafatawa har sauran maharan suka gudu.
Dangane da cewa an bayar da rahoton cewa wasu baki sun shiga Mahanga kuma basu dauki wani mataki ba sai kakakin STF yace babu wasu bakin da suka sani ko wani rahoto akan baki a Mahanga. Akan korafin da Fulani suka yi cewa an kashe masu shanu sai yace kwamandan STF ya je garin Mahanga din yayi taron sulhu da Fulanin wurin. Fulanin sun basu tabbacin cewa sun yafe abun da aka yi masu amma sun nemi taimakon rage masu asarar da suka yi. Kwamandan yayi alkawarin kai kukansu gaba. Ya umurcesu su zauna lafiya da kowa.
Kawo yanzu dai jami'an tsaro na cigaba da sintiri cikin daji koda zasu gano wasu cikin maharan.
Ga rahoton Zainab Babaji.