Gwamnatin tace bata gamsu da yadda suke gudanar da harkokin addininsu ba sabili da haka ta tarwatsasu daga sanasanin da suka kafa a karamar hukumar Lapai.
Mutanen da yawansu ya haura dari biyu sun kafa sanani ne a wani kauyen da suka sauya sunansa zuwa Medina. Tuni gwamnatin jihar tayi awon gaba da su tare da mayar da su garuruwansu na ainihi.
Alhaji Idris Ndaku sakataren gwamnatin jihar ya bayyana dalinsu na korar mutanen. Yace sun dauki matakin ne domin su cigaba da kiyaye harkokin tsaro a jihar. Duk abun da ka iya kawo fitina gobe to tun daga yau idan an gano shi a dakatar da shi, a kuma yi maganinsa. Abun da suka yi yanzu sun yi maganin abun da suke tsoro ka iya faruwa ne nan gaba.
Akan hadarin dake tafe da wadan nan mutanen Alhaji Idris Ndaku yace shugabansu yace shi malam ne kuma kodayaushe ya tashi sai ya dinga zagin mutane. Shugaban yana cewa duk sauran mutanen kafirai ne. Wai shi kadai ne malami har ma ya sawa kauyen Medina. Domin haka lamarin abun tsoro ne.
Shi ma sarkin Lapai Alhaji Umar Bago yace suna koyas da wani abu daban inda suna cewa iyayensu basu ne iyayensu ba kuma babu wani annabi sai malaminsu, wato shugabansu. Dalili ke nan ma suke kiran sansanin nasu Medina.
To sai dai mutanen basu saduda ba. Sun ce basu yadda da matakin korarsu ba. Sun sha alwashin garzayawa kotu akan lamarin. Alhaji Isiyaku Sammadi Lapai yayi magana a madadin mutanen. Yace sun riga sun shigar da kara a babban kotun jihar. Ya kuma hakikance cewa addinin musulunci suke koyaswa.
A can baya gwamnatin jihar Neja ta sha korar duk mutanen da bata gamsu da take-takensu ba akan yadda suke gudanar da harkokin addininsu. Baya bayan nan ta mayar da wasu Fulani jihar Kaduna.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.