Ya zama dole a zauna da makiyaya da manoma domin mutane ne dake zaune da cikin lumana da kwanciyar hankali amma yanzu kwatsam sai rikici ya barke tsakaninsu. Dalili ke nan da aka taru a zauna domin a san musabbabin matsalolin.
Bayan taron za'a ba gwamnati shawara akan abun da yakamata tayi.Akwai kuskuren da ake yi cewa duk makiyayi Musulmi ne manomi kuma ba Musulmi ba ne, to amma abun ba haka yake ba.
Hadiza Mustapha jakadiyar kasar Kamaru a Najeriya ta halarci taron tace abun dake akwai ba magana ba ce ta manyan mutane. Makiyaya da manoma suna nan. Za'a zauna dasu a sasanta, a kawo fahimta da daidaituwa domin kowa ya ji dadin rayuwa. Da manoma da makiyaya babu wanda zashi koina domin kasar tasu ce. Tace an kawo mutane daga kasashen Afirka daban daban domin su bayyana yadda suke kalubalantar rikicin makiyaya da manoma.
Alhaji Zubairu Jibrin Sarkin Gwari yana cikin sarakunan da suka halarci taron. Yace ya godewa Allah cewa gwamnatin tarayya ta san da matsalar dake tsakanin makiyaya da manoma. Tun da an mayar da matsalar magana ta kasa to an kamo hanyar warware matsalar.
Alhaji Muhammed Curuwa Zuru shugaban kungiyar Miyetti Allah ta Najeriya yace Fulani nada wasu hakkoki guda uku da yakamata gwamnati ta kiyaye masu. Na farko a bashi hanyar da zai bi da dukiyoyinsa ba tare da yiwa kowa barna ba. Na biyu a bashi inda zai zauna idan yayi kiwo. Na uku idan hukunci ya kamashi a yi masa daidai da abun da ya aikata.
Ga rahoton Lawal Ikara.