Takun Saka Akan Takarar Hama Amdou a Nijar

Hama Amadou

A Jamhuriyar Nijar wata sabuwar mahawara ta barke a game da makomar takarar jagoran ‘yan adawar kasar Hama Amadou.

Hakan na faruwa ne bayan da shugaban kotun daukaka kara ta birnin Yamai ya yi watsi da wata bukatar da lauyoyinsa suka shigar da nufin nuna adawa da hukuncin da aka yanke masa a shekarar 2017, bisa zarginsa da hannu a badakalar nan ta safarar jarirai.

Rashin gamsuwa da yadda aka yanke masa hukuncin zaman kurkuku na tsawon shekara 1 a yayin shari’ar da ta gudana a wani lokacin da yake gudun hijira a ketare ya sa jagoran ‘yan adawa Hama Amadou ta hanyar lauyoyinsa aikewa kotun daukaka kara wasika, wacce a cikinta ya nuna adawa da wannan mataki saboda a cewarsa abu ne da ya sabawa ka’idojin shari’a.

A amsar da ya bayar game da wannan bukata shugaban kotun, Gayakoye Abdourahamane, ya ce bakin alkalami ya riga ya bushe game da wannan shari’a ta badakalar jarirai.

Lauyan Moden Lunama, Me Daouda Samna

Sai dai a taron manema labaran da ya kira wani lauyan dan takarar jam’iyyar ta Moden Lumana, Me Daouda Samna, ya ce da kotu suke ja ba da shugaban kotu ba.

Wannan sabuwar dambarwa ta taso ne a wani lokacin da ake jiran jin matsayin kotun tsarin mulkin kasa a game da aikin tantance takardun mutanen da ke sha’awar shiga zaben shugaban kasa na watan disambar da ke tafe.

Kuma ana ganin hukuncin da aka yankewa Hama Amadou a watan Oktoban 2017 wani abu ne da ka iya gogawa takardunsa bakin fenti watakila ma ya shafi matsayinsa na dan takarar zaben da ake shirin gudanarwa a watan Disambar da ke tafe saboda haka lauya Me Daouda Samna ke kiran kotu ta yiwa jagoran na ‘yan adawa adalci.

A shekarar 2014 ne, hukumomin Nijar suka kaddamar da bincike bayan da wata jarida ta ruwaito labarin da ke cewa wasu manyan attajirai da ‘yan siyasa da jami’an gwamnatin Nijar na da hannu a wata badakalar safarar jarirai.

Wanda a cikinsu har da kakakin majalisar dokokin kasar, Hama Amadou, zargin da ya ce ba shi da tushe ballantana makama, hasalima makarkashiyar siyasa ce da aka kitsa takanas da nufin goga masa kashin kaji.

Yayin da gwamnatin Nijar ke cewa babu hannunta a wannan batu da ake alakantawa da shari’a.

Saurari cikaken rahoton Souley Moumouni Barma:

Your browser doesn’t support HTML5

Takun Saka Akan Takarar Hama Amadou a Nijar