Dubban magoya bayan jam’iyyun adawa na FRDDR da FP da FOI da kuma FDR ne suka hallara a dakin taro na palais du 29 juillet, domin jaddada goyon bayansu ga wannan sabuwar tafiyar da jagororin ‘yan hamayya suka sa gaba a karkashin jam’iyyar hamayya da suka kira Coalition pour une alternance democratique CAP 20 21.
A karkashin wannan sabon salo ‘yan adawar na hangen samun gagarumar nasara a zaben gama garin watan Disambar 2020, kamar yadda kakakinsu Mme Bayar Mariama Gamatche ta bayyana a wata sanarwa.
Dukkan wasu manyan shugabanin ‘yan adawa galibinsu ‘yan takara a zaben shugaban kasa mai zuwa ne suka jagoranci bukin kafuwar jam’iyyar hadakan, irinsu tsohon shugaban kasar Nijer Mahaman Ousman na jam’iyar RDR CANJI da tsohon Fra Ministan Hama Amadou na Moden Lumana da Ibrahim Yacouba na MPN Kishin kasa da Amadou Djibo Max na UNI da Amadou Boubacar Cisse na UDR TABBAT da dai sauransu.
A ci gaba da wannan gangami shugabanin kawancen na CAP 20 21 sun zarce da wani takaitaccen taron manema labarai, inda jagoran ‘yan adawa Hama Amadou ya sake tunatarwa game da yanayin da aka gudanar da zagaye na 2 na zaben 2016, wato lokacin da yake tsare a gidan yarin filingue a wani lokacin da ya kamata ya yi yakin neman zabe, a matsayinsa na wanda zai fafata da dan takarar PNSD na wancan lokaci wato Issouhou Mahamadou.
Domin karin bayani saurari rahotan Sule Muminu Barma.
Facebook Forum