Takaddamar Kwaskwarimar Kudin Tsarin Mulkin Nijar

NIGER: Taron Jam'iyyar MPN Kishin Kasa

Mataimakin shugaban jam’iyar MPN KIshin Kasa ta ‘yan adawa Korone Masani ya yi wa manema labarai karin bayani akan dokokin da suka haifar da rashin fahimtar da ta tilasta masu kaurace wa zaman kwamitin kwaskware kundin zaben Nijer .Batun kayyade yawan mutanen da za su tafiyarda harakokin hukumar zabe a matakin kasa da tsarin nada shuwagabanin hukumar a jihohi na daga batutuwan da suka haddasa rarrabuwar kawuna a yayin wannan zama, mafari Kenan da 'yan adawa suka fice daga wannan taro da a can farko aka yi zaton zai kawo karshen kiki kakar dake tsakanin bangaorin siyasar Nijer.

Kundin zaben kasar Nijar a sashensa na 8 ya yi haramcin shiga zabe ga duk wanda kotu ta yanke wa hukuncin daurin shekara guda a gidan yari saboda Haka 'yan adawa suka shawarci kwamitin ya sassauta zuwa shekaru 3 shawarar da masu rinjaye suka ce zai fi kyau a gabatar da ita gaban majalisar CNDP dalilin kenan da magoya bayan jam’iyar MODEN LUMAN ke ganin wannan a matsayin wani matakin datse wa shugabansu Hama Ahmadu hanyar shiga zaben shugaban kasa na 2021.

Ga wakilinmu a Yamai Sule Barma da cikakken rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

Nijer 'Yan Adawa Sun Fice Daga Zauren Taron Kwamitin Da aka Korawa Alhakin Kwaskware Kundin Zaben Kasar