‘Yan jarida da sauran jama’a a Janhuriyar Nijar sun kadu matuka da samun labarin rasuwar mace ta farko ‘yar jarida a kasar, wato Hajiya Maryama Keta, wadda ta rasu jiya Litinin a kasar Turkiyya, bayan shekaru 72 a duniya. Tuni aka shiga ta’ziyyar rasuwar wannan mace da ta kafa tarihi a bangaren aikin jarida da kuma gudunmowar da ta bayar ta fuskoki daban-daban a tsawon rayuwarta.
Cikin abubuwan da ake tunawa da marigayiya Maryama Keta har da yadda ta yi amfani da kwarewarta ta fannin jaridanci ta yi ta daukaka muradan mata da matasa, musamman ma a karkara. Cikin wadanda su ka fara bayyana bakincikinsu da rasuwar Maryama Keta har da Shugabar kungiyar Matan Afirka ta APAC Da Ke aikin Sadarwa, Hajiya Amina Niandou wadda ta ce, “Ni da kaina, a matsayin shugabar kungiyar ga, na yi rashin uwa saboda ta sha ba ni shawara game da aikin jarida, da yadda ake zama da mutane da kuma yadda ake zama da shugabanni. Kai, ‘yan jarida sun rasa uwa.”
Bayanin sanarwar da wakilinmu a Yamai Sule Mummuni Barma ya turo na cewa, “Allah ya yiwa tsohuwar shugabar hukumar sadarwar Jamhuriyar Nijer (CSC), Maryama Keita, rasuwa bayan da tayi fama da rashin lafiya na wani lokaci mai tsawo. Maryama Keita ita ce mace ta farko da ta fara aikin jarida a Nijer yayinda a daya bangaren ta sadaukar da rayuwarta wajen kare hakkin mata da yara kanana.”
Barma ya cigaba da cewa, “A shekarar 2003 Maryama Keita ta dare kujerar shugabancin hukumar sadarwa ta CSC har i zuwa shekarar 2007. A cewar shugaban hukumar ta CSC na yanzu Dr. Kabirou Sani dabi'un marigayiyar abin koyi ne ga kowa.
Jajircewa akan maganar 'yancin mata ya sa daukacin matan Nijer suka damkawa wannan tsohuwar 'yar jarida ragamar gamayyar kingiyoyin mata ta CONGAFEN a jajibirin tsundumar Jamhuriyar Nijer cikin tafarkin demokaradiyya.
'yar kimanin shekaru 72 da haifuwa, Maryama Keita ta shafe watanni kwance a babban asibitin Yamai kafin daga bisani aka fice da ita zuwa wani asibitin Istanbul na kasar Turkiyya, inda rai ya yi halinsa a jiya Litinin 29 ga Watan Oktoba.”
Ga wakilinmu a Yamai Sule Barma da cikakken rahoton:
Facebook Forum