Sake maido da kyaukayawar rayuwa wa jama’ar yankunan da matsalar tsaro ta afkawa a kasashe 5 mambobin kungiyar G5 Sahel shine abinda gwamnatocin wadanan kasashe ke hange ta hanyar hadakar kungiyoyin Alliance Sahel mai huldar aiki da manyan kungiyoyin duniya. Dalili kenan da wadanan bangarori suka hadu a Yamai da nufin duba yiyuwar gagauta kaddamar da ayyukan da talakawa zasu gani a kasa.
A karkashin wata yarjejeniyar da bangarorin suka cimma masu hannu da shuni sun amince zasu bayarda kudaden tafiyar da ayyukan dake kunshe a tsarin inganta rayuwar jama’a yayinda kasashen G5 Sahel suka jaddada aniyar tabbatar da doka da oda don baiwa talakawa damar samun walwala a duk inda suke.
A watan Disanba dake tafe shugabanin kasashen Mali da Nijar da Burkina Faso da Chad da Mauritania zasu gudanar da taron koli da zummar bibiya kan ayyukan da wannan taro ya bayarda shawara akansu, da kuma batun rundunar hadin guiwar G5 Sahel mai alhakin murkushe kungiyoyin ta’addancin da ke addabar jama’a akan iyakar Mali da makwaftanta.
Saurari Cikakken rahoton Souley Moumouni Barma
Facebook Forum