Machar ya isa birnin da safiyar jiya Laraba ta filin saukar jiragen sama na Juba, daga kasar Afirka ta Kudu domin ya halarci wani buki da abokin hamayyarsa Salva Kiir ya shirya.
Mutanen biyu dai sun sabunta yarjejeniyar sulhu da suka rattabawa hannu tun watan Satumba, don kawo karshen rikicin kasar da ya kwashe kusan shekaru biyar.
Machar dai ya taba zama mataimakin shugabanSalva Kiir bayan samun ‘yancin kai da kasar tayi daga Sudan a shekarar 2011, amma daga baya giyar mulki ta yi sanadiyar fada tsakaninsu da ya bayansu. Kiir da Machar dai sun yi ta sa hannu akan yarjeniyoyin sulhu barkatai, amma ba a cimma nasara ba. ciki har da ta shkearar 2016 wadda a sanadin barkewar tashin hankali a babban birnin Machar ya bar kasar.
Yakin basasar kasar yayi sanadiyar mutuwar kusan mutane 400,000 yayin da miliyoyi suka rasa muhallansu.
Karkashin sabuwar yarjejeniyar Machar zai rike mukamin mataimakin shugaban kasa na farko karkashin gwamnatin wucin gadi.
Facebook Forum