Gwamnatin Morocco ta karbi kudin Turai euro miliyon 160 domin yin amfani da sojojin yakinta wurin hana bulaguro bakin haure daga kudu da saharar Afrika zuwa Turai, lamarin dake kara yin yawa. Amma yanzu ‘yan kasarta sun karu a cikin masu amfani da kwalekwale suna ratsawa ta tekunta suna tsllake tekun Baharum.
Gwamnatin Morocco bata bada alakalumma a kan yawan ‘yan kasarta da suke barin kasar ta barauniyar hanya ba. Amma dai jami’an sojin ruwa da suke sintiri sun ce sun ga kwalekwale da dama suna ratsa karamin ruwan Strait of Gibraltar dake tsakanin Morocco da Spain cike makil da ‘yan Morocco, abin da suka ce yana karuwa a cikin wannan laokaci.
A cewar gwamnatin ta Madrid, bakin haure ‘yan kasar Morocco dubu 13 ne suka isa Spain a cikin watan Agusta, wani adadin da ba a taba samu ba, inji Mohammed Ali, wani dan rajin kare hakkin bil adama kuma mai bada shawara ga hukumar birnin Tetouan dake arewacin Morocco inda kananan jiragen ruwan bakin hauren ke tashi zuwa Turai.
Sojojin ruwan Morocco sun kashe wani dalibin karatun lauya mai shekaru 19 da haifuwa dan kasar kana suka raunata wani matashi yayin da suka bude wuta a kan kwalekwalen bakin hauren domin su tare su a wurare dabam-daban a watan da ya gabata, lamarin da ya yi sanadiyar wata gagarumar zanga zanga a garuruwar da wadanda harbin ya shafa suka fito da suka hada da Tetouan da Agadir
Facebook Forum