AFCON 2025: Ko Rashin Osimhen Zai Yi Tasiri A Wasan Najeriya Da Libya?

Super Eagles (Hoto: Facebook/Super Eagles)

Yanzu kocin Super Eagles Augustine Eguavoen zai dogara ne da ‘yan wasa irinsu Victor Boniface, Ademola Lookman, Taiwo Awoniyi da Kelechi Iheanacho don ganin Najeriya ta kai ga gaci.

‘Yan wasan Najeriya na Super Eagles za su kara da na Libya a ranar Juma’a a birnin Uyo da ke jihar Akwa Ibom a Najeriya.

Za a buga wasan ne a neman gurbin shiga gasar kofin nahiyar Afirka ta AFCON 2025.

Najeriya ce dai take saman teburinsu na D da maki hudu bayan da ta samu nasara a wasa daya sannan ta tashi canjaras a wasa na biyu.

Super Eagles ta yi nasara da ci 3-0 a wasanta da Jamhuriyar Benin yayin da tashi ba ci ko daya tsakaninta da Rwanda a birnin Kigali.

Najeriya za ta buga wannan wasa ba tare da zakukurin dan wasanta Victor Osimhen ba, saboda rauni da ya ji kamar yadda rahotanni ke cewa.

Yanzu kocin Super Eagles Augustine Eguavoen zai dogara ne da ‘yan wasa irinsu Victor Boniface, Ademola Lookman, Taiwo Awoniyi da Kelechi Iheanacho don ganin Najeriya ta kai ga gaci.

Ita dai Libya na can kasan teburin da maki daya. Ta tashi da ci 1-1 a wasanta na farko da Rwanda yayin da Benin ta doke ta a wasanta na biyu.