Sun Gudanar da Taron Bisa Umarnin Shugaba Buhari

Shugabat Muhammadu Buhari

Bisa ga umarnin shugaba Buhari, Gwamnonin arewa maso gabas sun gudanar da taro saboda matakan dawo da tsaro da farfado da tattalin arzikin yankin.

Jihohi ukku na yankin sun fi fuskatar hari ‘yan Boko Haram inda suma sauran ukkun ke samun nasu Kason da zama tundun mun tsira ga ‘yan gudun Hijira, Gwamna Muhammad Abubakar, na jihar Bauchi shi ya dauki bakuncin taron.

Kawar da shigayen binciken Sojoji bai yawaita a yankin na arewa maso gabas ba, da hakan bai rasa nasaba da tsaro, wasu ‘yan sa kai da suka hada da ‘yan banga da mafarauta, barayi na ganin lokaci yayi da za’a basu dama su bada tasu gudurmawar wajen samar da tsaro, masamman ma da lamarin ya hada da ‘yan fashi da makami, barayin Shanu da masu sace mutane don samun kudin fansa.