Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Harshe Da Karin Magana Tare Da Dr. Abdullahi Garba Imam


Dr. Abdullahi Garba Imam
Dr. Abdullahi Garba Imam

A cigaban shirin mu na Harshe da Karin Magana wannna makon ma muna tare da Dr. Abdullahi Garba Imam na kwalejin Aminu Kano dake Kanon Najeriya.

Wannan makon zamu duba Karin Maganar da ake mutunta dabba da kwaari, kamar dai yadda a baya Dakta Abdullahi yayi mana bayani akan Karin Magana da nau’o’insu, amma a wannan karon Dakta ya mai da hankaline kan Karin Maganar da ake mutunta Kwaro.

Ana ‘daukar kwaro a bashi wata ‘dabi’a ko suna ko kuma wani al’amari da aka san mutum ne keyi sai a bawa kwaro, missali ace “Dan banzan ko ya kula, wai kunama ta haifi kasko.” To anan an ‘dauki kunama an maida ita mutum, shi kuma kasko an san abune wanda yake baya motsi ko bashi da rai.

“Mu dai Allah yayi mana tafiya, wai kuda ya ga mai kilishi.” To idan aka duba wannan karin magana za’a cewa kilishi abune na sha’awa kuma na kwadayi, shi kuma kuda dai an sanshi da kwadayi inda ma ake cewa guda gurin kwadayi ake mutuwa.

Domin sauraron cikakkiyar hirar Dr. Abdullahi Garba Imam, danna sauti.

XS
SM
MD
LG