Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Duniyar Fina Finai Da Nazifi Abdussalam Yusuf


Dandalin VOA ya sami zantawa da Nazifi Abdussalam Yusuf wanda yai fice wajen yin wakokin Hausa da shirya fina finan zamani.

A cikin hirar wakiliyar Dandali Baraka Bashir da Mallam Nazifi ya bayyana mata cewa yana yin wakoki irin wadanda ake ji a cikin fina finai, haka kuma yana jin wakokin siyasa da na biki da ta ra’ayi da sauransu. Ya kuma fara waka tun a shekara ta 2001, kuma abinda ya janyo hankalinsa shine fahimtar sa ta cewa waka wata hanya ce ta aikawa da sako zuwa ko’ina a duniya, wadda take hanya mafi sauki wajen isar da sako.

Mallam Nazifi dai yayi wakoki masu ilimantarwa da dama inda ya bada missali da wata waka da yayi kan barace barace wadda har gwamnati ta yi amfani da ita wajen ilmantar da mutane.

Duk da yake dai bai cika yin wakokin sa ba a hotan bidiyo, yawancin wakokinsa yana yin su ne cikin sauti. Nazifi ya bayyana satar Fasaha a matsayin wani kalubale garesu, wanda yake tauye kasuwar su a fadin kasar, inda yayi kira ga gwamnati da ta shiga ta duba lamarin domin masu satar fasahar sunyi girman da sai gwamnati kadai zata iya yin maganin su.

XS
SM
MD
LG