Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gaskiya Matsalar Karuwa Yake yi a Tsakanin Matasa


A kalla mutane dubu hudu da dari bakwai ne suke fama da ciwon tabun hankali a jihar Borno, sakamakon shan miyagun kwayoyi da ya zama ruwan dare tsakanin matasa maza da mata.

Sansanonin ‘Yan gudun hijira dake zaman muhallin iyalen da ‘yan Boko Haram suka raba da gidajensu yanzu haka na fama da matsalar shaye shayen muggan kwayoyi.

Dr. Babagana Machina, Wani likitan masu tabun hankali ya shaidawa wakilin muryar Amurka, Haruna Dauda, cewa ana samun yawaitar masu fadawa cikin halin ta’ammali da miyagun kwayoyi, harda mata wadda yawansu ya kai kimani kashi goma sha bakwai cikin dari.

Ya kara da cewa kashi hamsin cikin dari na wadanda suke kwance a asibiti, duk matsala ce ta kwaya, yana mai cewa gaskiya matsalar karuwa yake yi, kashi saba’in cikin dari na wadanda suke da matsalar shaye shaye miyagun kwayoyi matasa ne, duk da cewa yanzu an fara samu yawaitar shaye shaye a tsakanin mata da kuma mutane da suka manyanta.

XS
SM
MD
LG