Cikin shirin mu na duniyar fina finai Dandalin VOA ya samu zantawa da Mallam Nafi’u Gwammaja wanda aka fi sani da Mogambo, mai yiwa jarumai kwalliyar tufafi da kula da jin dadin su.
A zantawar su da Baraka Bashir inda ya bayyana mata cewa shine ke zabarwa jarumai kayan da suke sakawa alokacin shirya wasan fim, ya dai kwashe shekaru goma sha takwas yana wannan aiki.
Mogambo dai yace rashin aikin yi ne da talauci sune makasudin shiga wannan harka, duk da yake yana da sha’awar wasan fina finai amma alkhairin da ake samu ciki shine babban abinda ya kara jan hankalin sa ga sana’ar. Mogambo dai bai je makaranta ba domin koyar wannan aiki, ya koya ne a gurin wani uban gidan sa mai suna Auwalu ‘Dan Dabara a Sarauniya wanda ya zamanto mataima kin sa kafin daga baya ya sami cin gashin kansa.
Burun Mogambo dai a wannan harka shine yana so yafi jarumi Ali Nuhu suna a hakar fina finai, kasancewar shine Jarumi da yafi kowa suna a yanzu haka.